Tsohon gwamnman jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce taron da PDP ta yi a jihohin Jigawa da Katsina ne ya firgita APC har shugabannin jam'iyyar suka roki Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya ayyana cewa zai sake yin takara.
A wata hira da ya yi da BBC Sule Lamido ya ce : ''Ai taron da aka yi a Jigawa da na Katsina shi ya firgita su, suka ce ranka ya dade gara fa ka zo, domin yadda aka yi taron nan na Jigawa da Katsina, idan ba ka zo ka ce za ka yi takara ba mun shiga uku...''
A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyyarsa ta kara tsayawa takara a zaben 2019.
TALLA
Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar
Saurari hirar da BBC ta yi da Sule Lamido
Tsohon gwamnan ya kara da cewa APC da Buharin sun yi hakan ne domin su samu dan hutu na ''Tsunamin'' da PDP ta yi a jihohin biyu a tarukanta.
Ya ce sai ma jam'iyyar tasu ta yi irin taron a Sokoto da Kaduna da Kebbi kafin kuma ta yi na Abuja lokacin da hankalin shugaban da jam'iyyarsa za su fi tashi.
Tsohon ministan harkokin wajen ya ce ba su da wata fargaba kan ayyanawar da Shugaban ya yi cewa zai sake yin takara.
"Domin ai 'yan PDP ne suka haife APC, saboda haka Buhari jikansu ne, kuma ''don zai yi takara mene ne abin damuwa?''
Sule Lamido ya ce tun da Buhari yake tsayawa takara sau uku ko hudu bai taba cin zabe ba.
Ya ce sai da gwamnonin PDP biyar da "wasu jiga-jiganta irin su Atiku da Wamakko da Goje da Abdullahi Adamu da Kwankwaso da Bukola da sauransu suka mara masa baya."
Kuma ya ce ko da ma Buharin zai sake takara ai wadanda suka mara masa baya ya ci zabe a yanzu sun bar APC sun koma gidansu PDP, don haka ba su da wata fargaba a kan takararsa.
"Domin daman shi a karan-kansa bai taba cin zabe ba," in ji shi
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Buhari's Social Investment Programs to NextLevel loading
We Will Expand N-Power, TraderMoni, MarketMoni, Others – OsinbajoPublished 1 hour ago on March 29, 2019 Vice President of Nigeria Professor ...
-
Bismillahir-rahmanirrahim From the letters of the Jurist Sīdī Muhammad Aknusūs, may Allah be pleased with him And know, O bother that no...
-
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU How to pray Salatul Tasbih – Method & Benefits Our Beloved Prophet Mohammed (SAW) o...
-
Senate writes off N1.5tr social investment project* The Senate Thursday rated the implementation of the N1.5triilion National Social In...
No comments:
Post a Comment