Daga Shafin #Bashir Ibrahim Na'iya
1.
YUNWA...... Chef BNG
Duk wani yanayi da zai gusawar da mutum hankalisa sakamakon karancin abinci (food insecurity) shi ne ma'anar yunwa. Abubuwan da suke kawo food insecurity/rashin wadatuwar abinci, suna da yawa, abu na fsrko shi ne, karancin ruwan sama na tsawon lokaci, da kwarin da ke lalata amfanin gona, da kuma canjawar yanayi dss. Shi kuwa food security, shi ne wadatuwar abinci mai kyau mai lafiya ga dukkan yan kasa. Kasar Ireland ce ta haye gurfin United States yanzu ita kasa ta farko a duniya ajerin kasashen da su ke kan matakin food security.
Food security, yana da matukar muhimmanci ga duk wata kasa dake duniyar nan, domin ana lura da shi sosai da sosai. Food security ba ya samuwa dole sai da taimakon ko tallafawar gwamnatin kowacce kasa, shi yasa harkar tsaro/security da food security, sune manyan aiyuka na farko da su ka rataya akan kowanne shugaban kasa. Ko a addinance wadannan abubuwan biyu tare suke tafiya wato "aminci da abinci/abinci da aminci".
Idan kun lura duk inda Shugaban kasar Najeriya Buhari yake yin wani muhimmin jawabi ga yan kasa sai kun ji ya kawo batun food security, hatta a jawabinsa na baya-bayan nan na ranar 29 ga watan May, sai da ya shugo da batun food security, tun hawansa mulki yake wannan maganar har zuwa yanzu....
"InshaAllah zan kammala rubutun zuwa karshe daga inda na tsaya a sama, za ku ga ci gaban post din da safe. Yanzu dai bakinku a bude yake ba wanda zai ce na sa masa rai yana azumi, lol"
2.
Tun daga lokacin da Buhari ya dare kan mulki kusan duk wani babban jawabi da zai yi sai ya sako batun food security. Muhimmancin hakan ne Gwamnatinsa ta shigo da tsarin ciyar da yara yan makaranta, sannan ake karfafa muhimmancin noma, amma abun mamaki har yanzu hakan bai cimma ruwa ba. Wani abu da zai baku mamaki shi ne, a nahiyar Africa, Najeriya ba ma ta cikin jerin goman farko na food-secure countries. Allah ya kyauta.
Idan muka koma kan batun dana fara yin magana akansa a post din farko wato "yunwa", abun akwai ban tsoro da tausayi. An ce a wuraren da ake rabon abinci na yan gudun hijra, wasu har ji musu ciwo ake, kai na so na ji an ce har asarar rayuka ake. Kwanan ma na ji an ce wani dansanda yana duka yana korar mutane saboda yawansu, amma wata mata tayi wata irin bajinta ta ruke bulalar, dansanda ya yi juyin duniyar nan ya kwace bulalar daga hannun matar amma ya kasa, duk fa a wajen rabon abincin. Wadannan abubuwan da suke faruwa, su suke tabbatarmin da cewa lallai in ba yunwa ba, to babu abin da zai gusarwa da mutum hankalinsa irin haka.
Shawara
Mutukar gwamnatin Najeriya da gaske take akan batun food security, to ga shawara, na san dai da wuya ku kanku ku yarda da yiwuwar shawarata balle kuma gwamnati. Shawarar tawa ita ce, ya kamata gwamnatin tarayya ta tallafawa manomanmu dari bisa dari, wato ina nufin cewa takin zamani/fertilizer da iri/seeds da kuma Agricultural mechanization/kayan aikin noma na zamani, duk su zama KYAUTA FREE OF CHARGE ga dukkan manoman mu da ke fadin Najeriya. Ni a ganina wannan ce kawai hanyar da zata dora kasarmu Najeriya akan gurbin food security. Na tabbata akwai kudin da za a iya yin hakan, domin duk kasashen da su ka ci gaba ta fannin food security suna samin babban tallafi daga gwamnatinsu, in ba haka ba tayaya shikafar da za a shigo da ita daga waje har ta fi sauki ko ya kasance bambanci kudinsu babu yawa da wacce ake nomawa a gida?
Na san dayawa za ku jinjina wannan shawarar ku ga kamar bazai yiwu ba saboda matsalolin da kasar ke ciki. Amma ni a ganina hakan zai yiwu sai dai in ba a gwada ba, in za sami jajurtattu kuma amintattun mutane, sannan a sami tsari mai kyau gami da dokoki ma su tsanani, to tabbas hakan zai yiwu. Muna da yara masu yawan gaske da su ka gama makaranta, to duk sai a kwashe su a basu aikin kula da rarraba takin da kuma kayan aikin noman na zamani, Wallahi kar ku yi mamakin sai ta kai ga aikin ne ma yake jiran yaran su gama karatu, ba wai sune za su yi ta neman aikin ba bayan sun kammala karatunsu. Ni a ganina wannan shi ne babban gatan da za a yi mana, kuma hakan zai yi wa kowa dadi a kasar. Domin kuwa abincin zai yi saukin da koda an shigo dana kasar wajen bazai fi namu sauki ba. Amma yanzu an hana a shigo da abincin sannan namu na gida bai isa ba, kun ga dole a samu yunwa mutane su fita daga hayyacinsu.
Gaskiya nima kamar ku, hakika hoton abincin nan yasa raina ya biya, amma ba damar ci, domin abincin gandai Al-Ameen ne, lol
Allah yasa mu dace, Allah ya raba mu da yunwa, Allah ya hore mana Ya bamu lafiyar nema.
Bashir Ibrahim Na'iya
Chef BNG
June 4th, 2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Buhari's Social Investment Programs to NextLevel loading
We Will Expand N-Power, TraderMoni, MarketMoni, Others – OsinbajoPublished 1 hour ago on March 29, 2019 Vice President of Nigeria Professor ...
-
Bismillahir-rahmanirrahim From the letters of the Jurist Sīdī Muhammad Aknusūs, may Allah be pleased with him And know, O bother that no...
-
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU How to pray Salatul Tasbih – Method & Benefits Our Beloved Prophet Mohammed (SAW) o...
-
Senate writes off N1.5tr social investment project* The Senate Thursday rated the implementation of the N1.5triilion National Social In...
No comments:
Post a Comment