Sunday, 2 December 2018

Bukola Saraki ya alakanta NPower da Siyan kuri'un Talakawa


Jam'iyyar Apc mai mulki a Najeriya ta musanta zargin cewa tana amfani da
shirin tallafi ga matasa da kananan 'yan kasuwa a matsayin wata dabara ta
saye kuri'unsu a zaben 2019.

Kakakin majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki kuma shugaban kwamitin
yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyar adawa ta PDP ne ya
yi wannan korafin.
Ya zargi APC cewa tana amfani da shirin bayar da tallafi a matsayin wata dabara
ta sayen kuri'un jama'a.

Saraki ya yi korafin cewa ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana
fakewa da shirin bayar tallafi ga kananan 'yan kasuwa yana zagaya wa yana
karbar katinan zaben jama'a.

Amma a martaninta gwamnatin Buhari ta musanta zargin inda Dakta Bilkisu
Sa'idu mataimakiya ta musamman ga mataimakin shugaban kasa ta ce babu
inda ake tambayar wadanda ake ba tallafin jam'iyyar da suke goyon baya.
Ta ce babu inda ake tambayar mutum katin zabe kafin a ba shi tallafin.
"Wannan maganar ba ta da tushe bale makama, domin shiri ne na 'yan kasa, ba
na wani bangare guda ba," in ji ta.

Kwanakin baya dai 'Yan majalisa sun bukaci dakatar da N-Power a cewar su 'Ba da zuciya daya gwamnati ke raba kudin tallafi ba'

Saraki ya ce tun kaddamar da shirin a 2015, sai a yanzu a 2018 mataimakin shugaban kasar ke zagaya wa yana raba wa kananan 'yan kasuwa kudi don sauya ra'ayinsu.
Kuma ya ce APC ta mayar da shirin a matsayin nata ita kadai, inda ya ce
"mataimakin shugaban kasar na tafiya tare da shugabar mata ta jam'iyyar APC ba tare da wakilan sauran jam'iyyun siyasa ba."

"Kudi ne na 'yan kasa ba na APC ba", in ji Saraki.
Ya ce kudaden tallafin na cikin lassafin kasafin kudi tun na 2015.
Sai dai kuma Dakta Balkisu ta ce sai a 2016 gwamnati ta kaddamar da shirin
bayar da tallafin da ake kira N-Power sabanin 2015 da Saraki yake ikirari.
Shirin na gwamnatin Buhari dai ya shafi bayar da tallafi ga matasa da ba su da
aikin yi da kuma bayar da tallafi ga kananan 'yan kasuwa.

No comments:

Buhari's Social Investment Programs to NextLevel loading

We Will Expand N-Power, TraderMoni, MarketMoni, Others – OsinbajoPublished 1 hour ago on March 29, 2019 Vice President of Nigeria Professor ...