Monday, 29 October 2018

GWAMNATIN TARAYYA ZATA DAUKI SABABIN MA'AIKATAN NPOWER BANGAREN WADANDA SUKA GAMA SECONDARY

Gwamnatin tarayya ta samar da shirin NPower domin samar da aiki ga matasan Nijeriya, da kuma koyawa musu sana'o'in dogarao dakai, gwamnatin ta bayyana a niyyarta na sake daukan sababbin ma'aikata a karkashin shirin Npower Build, ma'ana sashen koyar da sana'o'i da suka shafi harkar gini. Za a bude wannan kafa a tsakanin 5 ga watan Nuwamba zuwa 16 na wannan shekara 2018.
Ga duk mai sha'awa zai shiga www.npower.gov.ng domin yin rijista, bangarorin da za a dauka sune kamar haka;
1. Automobile (Gyaran mota)
2. Agric Tech (gyaran naurori da motocin Gona)
3. Plumbing (aikin ruwan famfo)
4. Carpentry & joinery  (kafinta da dukanci)
5. Masonry & Tiling (sa tile din kasa da bango)
6. Electrical Installation (hada wutar lantarki)
7. Hospitality (bude ido)

Shi wannan sashin ba kamar NPower graduate ba, shekara daya ake ana biyanka dubu goma (10,000) tare da samun kwarewar da zaka dogaro da kanka.

No comments:

Buhari's Social Investment Programs to NextLevel loading

We Will Expand N-Power, TraderMoni, MarketMoni, Others – OsinbajoPublished 1 hour ago on March 29, 2019 Vice President of Nigeria Professor ...