Wednesday, 14 November 2018

HUKUMAR HISBAH TA KANO TA AA KAFAR WANDO DAYA DA MASU RAWAR MALDWEBE


Daga BBC HAUSA
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta kama duk wanda aka samu yana taka sabuwar rawar 'fadi ka mutu' da ake yayinta a yanzu.
Ranar Talatar da ta gabata ne wani bidiyo ya fito da ke nuna wasu 'yan mata sanye da hijabi na tikar rawar da ta samo asali daga kasar Afirka ta Kudu.
Wasu mutane sun ce 'yan matan da ke cikin bidiyon 'yan jihar Kano ne, amma kakakin hukumar Hisbah a Kano, Adamu Yahaya ya shaida wa BBC cewa ba su samu wani rahoto mai kama da wannan ba.
"Gaskiyar maganar ita ce ba mu da masaniya game da wannan sabuwar rawar da ka ke magana a kai, amma aikinmu ne hana aikata laifuka masu bata al'adu da tarbiyyar al'umma.
"Saboda haka idan muka sami rahoton da ke cewa wasu na yin irin wannan rawar, to ko shakka babu za mu kama su".
Wannan sabuwar rawar ta samo asali ne daga wata waka da mawakin Afirka ta Kudu, King Monada, ya rera mai suna 'Maldwedhe' da aka ce tana caza kwakwalwar matasa.
Ma'anar kalmar Maldwedhe ita ce cuta, kuma Monada ya yi amfani da kalmar ce dangane da wani maras lafiya da ke dauke da cutar wadda ke sa shi ya suma idan ya kama masoyiyarsa tare da wani.

Ko a farkon shekarar 2017 ma an fito da sarar wata sabuwar rawa da matasa suka dinga yayinta a Najeriya, wato rawar dab, inda suke yi tamkar masu ruku'u su kuma rufe fuskarsu da hannu daya.
A wancan lokacin ma an yi ta ce-ce-ku-ce a kan wannan dabi'a.

No comments:

Buhari's Social Investment Programs to NextLevel loading

We Will Expand N-Power, TraderMoni, MarketMoni, Others – OsinbajoPublished 1 hour ago on March 29, 2019 Vice President of Nigeria Professor ...